Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A safiyar jiya Lahadi 8/6/2023 Kwamandan Rukunin Yaki na 86 na Dakarun Sojojin Ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da jami'ansu da iyalansu sun gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khamene'i wanda ya jinjina mai girmamawa ga ayyukan da Rundunar ta 86 ta cimmawa. Jagoran ya ce wannan rundunar jirgin ruwa ta tabbatar da cewa tekun ruwan 'yantacce ne ga kowa, kuma juyin juya halin Musulunci ne ya ba mu kwarin guiwar tafiya cikin teku.
A jiya lahadi da safe 8/6/2023 jagoran juyin juya halin musulunci Imam Khamenei ya gana da jagororin sojojin ruwa da ma'aikatan jirgin ruwa na 86 da iyalansu. Jagoran ya yi la'akari da cewa nasarar da wannan kungiya ta sa a gaba wajen zagayawa a duniya shi ne "sakamakon tsayuwar daka, da gwagwarmaya, da amincewa da kai, da tsare-tsare mai karfi, ilmin soja na ci gaba, gudanarwa mai inganci, jajircewa da tsayin daka wajen tinkarar kalubale ga matsaloli."
Kuma Imam Khamenei ya ce: Har yanzu wannan gagarumin yunkuri ya tabbatar da cewa nasarori, da nau'ikan ci gaba, da fatan da ake samu, suna fitowa ne daga zuciyar jajircewa, da gwagwarmaya, da jurewa wahala.
Hakazalika, Jagoran ya dauki cewa tafiyar cikin ruwa ta kilomita 65,000 a cikin kimanin watanni takwas abu ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran. Ya ce, "Wannan yunkuri mai ma'ana kuma mai zurfi bai kamata a yi la'akari da shi a matsayin aikin soji da na ruwa kawai ba, domin duk wani abin da ya haifar da shi ya cancanci kulawa da daukar darasi."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki yunkuri na dakarun sojojin ruwa ta 86 a matsayin cikar fadin Alkur'ani mai girma: {Ku shirya musu duk wani karfi da za ku iya}. Ya ce, “Ayyukan ku sun daga matsayin aikin soja na kasar nan, tare da karfafa taken ‘Mu Zamu Iya’, wanda shi ne ginshikin ci gaban da kasar nan da ta samu a bangaren rundunar soji da kuma kwakwale.
Jagoran ya fayyace sakamakon da wannan ayar take bayarwa da cewa: “Jin rauni, kokwanto, da rudani, duk suna haifar da kwadaitar da makiya su kai farmaki da daukar mataki, amma idan wani ya ga shiri da iyawa sai ya sake duba lissafinsa.
Imam Khamenei ya jaddada cewa wannan tukin jirgin ruwa na alfahari ya kuma inganta kimar Iran a duniya, kuma darajarta ta siyasa ba ta gaza ta soja ba, sannan ya tabo wasu darussa daga wannan shiri.
Yayin da yake ishara da kebantattun siffofi na teku da girmansa a matsayin abun da ke nuni ga ayoyin Ubangiji, Jagoran ya dauki sanin Allah a matsayin darasin farko na wannan tafiyar teku. Har ila yau ya ambaci wani darasi wanda shi ne juyin juya halin Musulunci: “A lokaci wanda yake mai abin kunya na zamanin Pahlawi da na Kajar, duk da yawan bakin teku da karfin ruwa, babu wani ilmi game da teku da karfinsa a kasar, a maimakon haka, sojojin ruwa ne sun shagaltu da wasu al'amura, amma juyin juya halin ya fitar da teku da tafiya acikinsa daga wani hali na tabarbarewar mantuwa da ya shiga."
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi imanin cewa kasancewar sojojin ruwa a yankuna masu nisa da kuma mafi nisa na tekun Pasifik da Atlantic wani lamari ne da ke samar da tsaron kasar. A daya bangaren kuma ya ce: “mamaya da kwace na kayan anfanin dan Adam wani bangare ne na sifofin Amurka da manyan kasashen duniya, kuma idan har za su iya, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yi wa tekunan rajista da sunayensu su ma, domin dakile su daga barin kaiwa ga wasu”.
A cikin wannan mahallin, Jagoran ya ci gaba da cewa: “Kun tabbatar da kasancewarku da fuskantar mugayen ayyukansu domin dakile ko murguda wannan tafiya cewa tekun budadden abu ne na kowa.
Dangane da wasu matsaloli da Amurkawa ke kawo cikas a harkokin sufuri da sufurin jiragen ruwa, Imam Khamenei ya ce: “Maganarsu da suke cewa ba za mu bari jiragen ruwa na su wane su bi ta ruwa su bi mashiga kaza ba" wannan wauta ce, domin budadden ruwa na kowa ne Dole ne tekuna da sararin samaniya su kasance 'yanci ga kowane al'umma, kuma dole ne a samar da tsaro na zirga-zirga da sufurin ruwa ga kowa.
Kuma Jagoran ya ci gaba da cewa: "A yau, Amurkawa suna kai hari kan jiragen dakon mai tare da bayar da taimako ga gungun masu safarar ruwa a yankinmu da sauran wurare, kuma wadannan ayyuka manyan keta dokokin kasa da kasa ne da na dan Adam."
Har ila yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin rawar da iyalai suke takawa a matsayin "muhimmiyar nasara wajen cimma nasarar aikin rundunar sojan ruwa ta 86." Ya ce, “Hakuri da juriya a cikin damuwa da buri, da alfahari a wannan jarrabawa da kuma nuna alfahari a tsakanin iyaye mata, maza da mata, wani abu ne mai matukar tasiri wajen cimma wannan yunkuri na tarihi.
Jagoran ya kara da cewa: “Shaukin iyalan sojojin ruwa ya kare da ganin ‘yan uwansu, amma ba zaa iya cika sararin shauki na ‘yan uwa na iyalan shahidan ba. Dukkanmu suna bin mu bashi, kuma muna rokon Allah da kada ya cire inuwarsu daga kawunan al'ummar Iran."
A wani bangare na jawabin nasa, Imam Khamenei ya yi ishara da tarukan makoki na watan Muharram na wannan shekara yana mai cewa: Duk da kokarin da makiya suke yi da kokarin ganin watan Muharram na bana, tare da kokarin ganin watan ya zama mara muhimmanci amma a wannan shekarar da albarkacin nunin Baqiytullah, sabanin buri. makiya, Ashura ta kasance mafi kwarjini da daukaka, da cin gajiyar shekarun da suka gabata, wanda hakan ke nuni da cewa Allah a kodayaushe yana taimakon kowane aiki bisa tafarkin hadafin Ubangiji.
A farkon wannan taro, kwamandan sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Admiral Shahram Irani, da kwamandan rundunar sojin ruwa ta 86, Admiral Farhad Fattahi, sun ba da rahoto kan aikin zagayen da sukai.
Hakazalika, a cikin wannan taron, matar ɗaya daga cikin membobin Rundunar Sojan Ruwa ta 86 ta rera yabo daga zuciya game da "buri, haƙuri da jinjinawa ta alfahari tsakanin iyalan Rukunin Rundunar Sojan Ruwa a lokacin aikin."